• Nijar Ta Sake Fatali Da Bukatar Italiya Na Jibge Mata Sojoji

 A Karo na biyu, gwamnatin Nijar ta ki amuncewa da bukatar kasar Italiya na jibge sojojinta a cikin kasar ta Nijar.

Ministan cikin gida na Nijar ne, Bazoum Mohamed ya bayyana hakan a wata hira da gidan radiyo kasa da kasa na Rfi.

Italiya dai na bukatar aike wa da sojojinta 470 a kasar ta Nijar don yaki da kwararar bakin haure da ta'addanci.

Kafofin yada labaren Italiya sun ce kin amuncewar Nijar kan wannan bukata babban kalubale ne ga kasar ta Italiya, a kokarin da take na yaki da kwararar bakin haure dake son shiga turai.

A watannin biyu da suka gabata ma dai, ma'aikatar harkokin wajen Nijar ta yi fatali da irin wannan bukata daga Italiya.

Tags

Mar 13, 2018 05:53 UTC
Ra'ayi