• Zaben Saliyo: Za a Sake Kirga Kuri'un Wasu Mazabu Kafin Sanar Da Sakamakon Karshe

Hukumar zaben kasar Saliyo (NEC) ta ce za ta sake kirga kuri'un da aka kada a wasu mazabu 72 na kasar a daidai lokacin da take fatan za ta sanar da sakamakon zaben na karshe a wani lokaci a yau din nan Talata.

A wata sanarwa da ta fitar a daren jiya Litinin, hukumar zaben ta ce har ya zuwa yanzu dai ba a soke wata kuri'a daga cikin kuri'oin da aka kada  a kasar ba, tana mai cewa kawai dai abin da hukumar za ta yi shi ne sake kirga kuri'un wasu karin mazabu 72, baya ga wasu 82 da a baya aka tsara za a sake kirgawa din don tabbatar da cikakken sakamakon zaben.

Har ya zuwa yanzu dai al'ummar kasar suna jiran sakamakon kimanin kashi 25% na kuri'un da aka kada din bayan da a baya hukumar zaben ta sanar da kashi 75% na zaben inda babbar jam'iyyar adawa ta Sierra Leone People’s Party (SLPP) ta ke kan gaba da jam'iyyar All Peoples Congress (APC) mai mulki.

To sai dai duk da hakan ana ganin zaben zai kai ga zagaye na biyu bisa la'akari da cewa babu wata jam'iyya da ta sami kuri'ar da ake bukata wajen lashe zaben a zagayen farko.

Tags

Mar 13, 2018 11:18 UTC
Ra'ayi