• Wasu Mahara Sun Kashe Jami'an Jamdarma 3 A Nijer

Wasu mahara kan babura sun kai hari kan jami'an tsaron Jandarma na Nijer a karamar hukumar Ouallam na jahar Tilabery tare da kashe uku daga cikinsu

Kafar watsa labaran Afirta Time ta nakalto gidan radion Sarauniya ta kasar Nijer na cewa a marecen jiya litinin wasu mahara kan babura dauke da manyan makamai sun kai hari kan shingen  jami'an tsaron Jandarma na kauyen Goubé dake karamar hukumar Ouallan na jahar Tillabery dake yammacin kasar.

Rahoton ya ce maharan da ba a kai ga gano ko su waye ba sun kashe jami'an jandarma uku tare da jikkata wani na daban, garin Goubé dai na da nisan kilomita kimanin 40 daga arewacin Yamai babban birnin kasar.

Rahoton ya ce a yayin da maharan suka kai hari, bayan wasu mintoci, jami'an jandarman sun samu dauki na karin jami'an tsaron, lamarin da ya sanya maharan suka gudu zuwa kasar Mali.

Duk da cewa har yanzu gwamnati ba ta fitar da sanarwa a hukunce ba, kuma ba a tattance mharan ba, to saidai al'umma na ganin cewa maharan 'yan ta'adda ne masu da'awar jihadi dake kan iyakokin kasashen Nijer da Mali, domin sun sabawa kai irin wannan hari na ta'addanci a kan jami'an tsaron kasar ta Nijer.

Tags

Mar 13, 2018 19:03 UTC
Ra'ayi