• Matsalar Rashin Aikin Yi Musamman A Tsakanin Matasa A Kasar Moroko

Tashar talabijin ta France 24 ta bada labarin cewa: Matsalar rashin aikin yi a Moroko ta yi kamari musamman a tsakanin matasan kasar.

Tashar talabijin ta France 24 ta watsa labarin cewa: Matsalar rashin aikin yi tana kara yin kamari a Moroko musamman a tsakanin matasan kasar, inda a kullum ake samun matasa suna zagaya ma'aikatun gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu domin neman aikin yi.

Abdul-Ghaniy Yumi masanin harkar tattalin arziki a Moroko ya bayyana cewa: Babban dalilin da ke kara janyo rashin aikin yi a tsakanin matasa a kasar shi ne; mafi yawan matasan Moroko ba su karatu a fannin koyon sana'o'i, don haka idan suka kammala karatu suke neman aiki a ofisoshi, kuma babu wata sana'a da suka iya ballantana su dauki matakin bude wajajen gudanar da ayyukan hannu domin dogaro da kai.

An kiyasta cewa a duk shekara jami'o'in Moroko suna yaye dalibai kimanin 130,000 a fannonin ilimi daban daban lamarin da ke kara janyo yawaitar matasa marassa aikin yi a kasar.

Mar 14, 2018 06:28 UTC
Ra'ayi