• Kokarin Ganin Shugaban Burundi Ya Ci Gaba Da Zama A Kan Karagar Mulkin Kasar

Jam'iyya mai mulki a Burundi ta bukaci gudanar da zaben raba gardama domin bada dama ga shugaban kasar Pierre Nkurunziza ya ci gaba da mulki har zuwa shekara ta 2034.

Babban sakataren jam'iyya mai mulki ta CNDD-FDD a kasar Burundi Evariste Ndayishimiye ya bayyana shugaban kasar Pierre Nkurunziza a matsayin shugaban da yafi dacewa ya ci gaba da mulkin kasar na tsawon lokaci sakamakon zurfin tunaninsa tare da jaddada yin kira ga magoya bayan jam'iyyar kan amincewa da wannan shawara.

A nashi bangaren Agathon Rwasa mataimakin shugaban Majalisar Dokokin Kasar Burundi kuma shugaban jam'iyyar adawa ta kasar ya bayyana rashin amincewarsa da wannan shawara; Yana mai fayyace cewa irin wannan gurguwar shawara zata wurga siyasar Burundi cikin mummunan kangi da rashin makoma.

Tuni dai jam'iyya mai mulki a Burundi ta gabatar da shawarar gudanar da zaben raba gardama domin neman amincewa da gudanar da gyarar fuska a kundin tsarin mulkin kasar da nufin bai wa Pierre Nkurunziza damar ci gaba da mulki har zuwa shekara ta 2034. 

Mar 14, 2018 06:30 UTC
Ra'ayi