• Hukumar Zaben Saliyo Ta Sanar Da Ranar Gudanar Da Zagaye Na Biyu Na Zaben Shugaban Kasar

Hukumar zaben kasar Saliyo ta tsayar da ranar 27 ga watan Maris na da muke ciki a matsayin ranar da za a gudanar da zagaye na biyu na zaben shugaban kasar bayan da ta sanar da sakamakon karshe na zagayen farko na zaben da aka gudanar a ranar 7 ga watan Maris inda babu dan takarar da ya sami kuri'un da ake bukata na ya lashe zaben a zagayen farko.

Bisa za sakamakon karshe na zaben da hukumar zaben ta fitar a yammacin jiya Talata, babbar jam'iyyar adawa ta Sierra Leone Peoples Party (SLPP) ce ta lashe zaben da sama da kuri'u miliyan 1.1, sai kuma jam'iyyar All Peoples Congress (APC) mai mulki wacce ta zo na biyu. To sai dai bisa la'akari da cewa babu guda daga ciin 'yan takaran biyu da ya sami kashi 55% na kuri'un da aka kda din da ake buka, don haka wajibi ne 'yan takaran biyu su je ga zagaye na biyu da za a gudanar makonni biyu bayan sanar da sakamakon zaben.

Wannan dai  shi ne karo na biyu da dan takaran jam'iyyar adawa ta SLPP din Julius Maada Bio ya ke kokarin darewa karagar mulkin kasar Saliyon bayan da ya sha kare a hannun shugaban kasar mai barin gado Ernest Bai Koroma a 2011. A baya dai ya taba rike shugaban kasar Saliyon a matsayin shugaban mulkin soji.

Masu sanya ido kan zaben dai sun ce an gudanar da shi cikin inganci da kuma kwanciyar hankali.

Tags

Mar 14, 2018 11:06 UTC
Ra'ayi