• Shugaban Kasar Zimbabwe Ya Maida Martani Kan Furucin Robert Mugabe

Shugaban kasar Zimbabwe ya maida martani kan furucin da tsohon shugaban kasar Robert Mugabe ya yi na cewa sauke shi daga kan karagar shugabancin kasar Zimbabwe yana matsayin juyin mulki ne a kasar.

A jawabin da ya gabatar a yau Juma'a: Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya maida da martani kan furucin tsohon shugaban kasar Robert Mugabe yana mai fayyace cewa; Gwamnatin Mugabe ta zo karshe a Zimbabwe kuma babu batun dawowarta.

A jiya Alhamis ce Robert Mugabe ya yi furuci da cewa hanyar da aka bi wajen sauke shi daga kan karagar shugabancin Zimbabwe bata da bambanci da juyin mulki, don haka ya yi tofin Allah tsine kan wannan salo.

Tun a watan Nuwamban shekarar da ta gabata ta 2017 ce sojojin Zimbabwe da jam'iyya mai mulki a kasar ta ZANU-PF suka bukaci Robert Mugabe da ya yi murabus daga kan karagar shugabancin kasar ta Zimbabwe ko kuma a dauki matakin tsige shi, inda ya amince da yin murabus, kuma aka maye gurbinsa da tsohon mataimakinsa Emmerson Mnangagwa.

Tags

Mar 16, 2018 19:28 UTC
Ra'ayi