Mar 17, 2018 06:31 UTC
  • Za A Gurfanar Da Zuma Kan Zargin Rashawa

Mai Gabatar da kara a kasar Afirka ta kudu ya ce za’a gurfanar da tsohon shugaban kasar Jacob Zuma a gaban kotu, domin tuhumarsa da laifufukan da suka shafi cin hanci da rashawa lokacin da yake rike da shugabancin kasar.

Babban  jami'i mai shigar da kara, Sean Abrahams  ya ce tsohon shugaban mai shekara 75 da haihuwa zai fuskanci shari'a akan laifukka 16 da suka shafi zamba, halasta kudin haram da cin hanci da rashawa.

Tuhume-tuhumen da ake masa sun hada da cewa ya karbi wasu kudaden haram gabanin zamansa shugaban kasa, kuma an tuhumarsa da cewa a shekarun 1990 ya nemi wani kamfanin kera makamai na Faransa da  ya rika daukar nauyin bukatunsa.

Jacob Zuma ya shafe shekaru yana watsi da  tuhumar cin hanci da rashawa da ake yi masa, kuma lauyoyinsa sun rika daukaka kararrakin da ak yi a kansa cikin nasara.

A yanzu dai gwamnatin ce za ta ci gaba da biyan kudaden da Mista Zuma zai bukata a wajen wannan shari'ar, kuma idan aka same shi da laifi, sabon shugaban kasar yana iya yafe masa.

Amma duk da hakan, wannan wani babban kalubale ne ga jam'iyyar ANC da take son nuna cewa ta juya wa dukkan batutuwan cin hanchi da rashawa baya gaba daya.

Tags

Ra'ayi