Mar 17, 2018 12:20 UTC
  • Togo: An Bude Taron Fada Da Ci-Rani

Taron da aka bude a babban birnin Togo, Lome, shi ne karo na 10 da kasashe masu magana da harshen Faransanci suke yi

Kamfanin dillancin labarun Xinhua na kasar Sin ya ambato shugaban Majalisar dokokin kasar Togo, Dama Dramani yaana cewa; Muhimman batutuwan da su ka shafi nahiyar Afirka da su ka kunshi yin hijira ba bisa ka'ida ba, suna daga cikin batutuwan da suke jan hankalin dukkanin cibiyoyi da kungiyoyi da kuma gwamnatocin nahiyar ta Afirka.

 Dama Dramani ya kara da cewa; Da zarar an kaddamar da shawarwari da ra'ayoyin da aka bijiro da su a gaban cibiyoyin da suka dace, to shakka babu za a sami sakamako mai kyau akan batun gudun hijirar.

Shi kuwa shugaban Majalisar kasar Cote De Voire Guillaume Soro wanda yake halartar taron na Lome ya ce; Fiye da kowane lokaci, batun yin hijira ba bisa ka'ida ba, yana damun nahiyar ta Afirka. 

A ranakun alhamis da jiya juma'a ne dai aka yi taron na Lome dangane da hijira ba bisa ka'ida ba.

Tags

Ra'ayi