• An Bude Zaman Taron Kasa Da Kasa Kan Karfafa Gwiwar Mata A Fagen Siyasa A Kasar Aljeriya

An bude zaman taron kasa da kasa kan karfafa gwiwar mata domin taka gagarumar rawa a fagen siyasa a birnin Aljes fadar mulkin kasar Aljeriya.

A sakon jawabin shugaban kasar Aljeriya Abdul-Aziz Boutafliqa da ministan ma'aikatar shari'ar kasar Attayyib Lauh ya karanta a madadinsa a yayin bude zaman taron a jiya Asabar: Jawabin ya yi nuni kan yadda mata suka taka gagarumar rawa a fagen samarwa kasar Aljeriya 'yancin kai daga turawan mulkin mallakar Faransa tare da jaddada bukatar ganin mata sun shigo an dama da su a dukkanin harkokin tafiyar da kasar ta Aljeriya.

Sakon shugaban kasar ta Aljeriya ya kuma kunshi aniyar gwamnatin kasar ta karfafa harkokin mata tare da gudanar da gyarar fuska a kundin tsarin mulkin Aljeriya domin bai wa mata damar taka gagarumar rawa a harkokin tafiyar da kasar. 

Tags

Mar 18, 2018 06:30 UTC
Ra'ayi