Mar 18, 2018 16:14 UTC
  • Sudan Da MDD Sun Cimma Yarjejeniyar Ficewar Dakarun Tabbatar Da Zaman Lafiya Daga Darfur

Gwamnatin Sudan da Majalisar Dinkin Duniya sun cimma yarjejeniyar dangane da fara aiwatar da matakin farko na ficewar sojojin tabbatar da zaman lafiya na majalisar da suke yankin Darfur zuwa karshen watan Yunin wannan shekarar.

Kamfanin dillancin labaran kasar Sudan ya jiyo Omar Dahab, jakadar kasar Sudan na dindindin a Majalisar Dinkin Duniyar yana fadin cewa za a fara aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin bangarori biyu a shekarar bara ta 2017 dangane da janye sojojin hadin gwiwa na MDD da kuma na Tarayyar Afirka da suke yankin Darfur da nufin tabbatar da zaman lafiya a karshen watan Yuni nan mai zuwa.

Jakadan na Sudan ya ci gaba da cewa a karshen watan Yunin, Kwamitin Tsaron MDD zai zauna don duba lamarin janyewar kana kuma daga nan ne za a dau matakin fara aiwatar da mataki na biyu na yarjejeniyar.

Jami'in na Sudan ya karasa da cewa matakin janye dakarun tabbatar da zaman lafiyan dai ya biyo bayan irin yadda aka sami kyautatutuwar yanayi ne a yankin na Darfur da ya fuskanci matsalar yakin basasa sakamakon bulla 'yan tawaye a yankin.

Tags

Ra'ayi