• Madagascar: Mahaukaciyar Guguwa Ta Ci Rayukan Mutane 17

Sanarwar da ta fito daga ofishin kula da bala'oi na dabi'a a kasar ya ce; Guguwar mai karfi da ta kada a kasar ta shafi mutane dubu 15.

A ranar juma'ar da ta gabata ne dai guguwar ta fara kadawa daga tsibirin Masuwwala da ke arewa maso gabashin kasar, san nan ta kada zuwa kudancin kasar a ranar asabar.

A cikin shekaru 10 na bayan nan Kasar ta Madagascar tana fama da guguwa mai karfi har sau 40.

A cikin watan Janairu na bana, wata guguwar mai taken "Awa" da ta kada a cikin kasar ta dauki rayukan mutane 51 da kuma batar da wasu mutanen 22.

A watan Maris ta 2017 wasu mutane 78 ne suka rasa rayukansu saboda guguwar.

Mar 19, 2018 12:14 UTC
Ra'ayi