• MDD Ta Mai da Martani Akan Sace Mai Shigar Da Kara Na Sojan Kasar Libya

Kamfanin dillancin labarun Xinhua na kasar Sin ya ambato majiyar MDD tana nuna damuwarta matuka akan garkuwa da babban mai shigar da kara na sojan kasar Libya, Mas'ud Arhumah.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira da a kare lafiyar Arhumah, tare da bayyana sace shi a matsayin cutar da tsarin sharia da tsaro na kasar ta Libya.

A ranar alhamis din da ta gabata ne aka sace Arhumah a kofar gidansu da yake a cikin birnin Tripoli. Kawo ya zuwa yanzu babu wata kungiya wacce ta sanar da daukar alhakin garkuwa da shi.

Hukumar kare hakkin bil'adama ta kasar Libya ta ce garkuwa da aka yi da babban mai shigar da kara na sojan Libya, cin zarafin harkokin shari'a ne, kuma wajibi ne a gano shi tare da hukunta masu hannu a ciki.

Tags

Mar 20, 2018 12:06 UTC
Ra'ayi