• Musulmi Sun Gudanar Da Zanga-Zanga A Kasar Afirka Ta Tsakiya

Al'ummar musulmin birnin Bangui na kasar Afirka ta tsakiya sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin jin dadinsu kan yadda ake ci gaba da kai musu hare-haren ta'addanci a kasar

Tashar Talabijin din France 24 ta habarta cewa wasu musulmi a birnin Bangui dauke da gawawaki 17 sun gudanar da zanga-zanga har zuwa babban ofishin dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD domin nuna rajin jin dadinsu kan yadda rikici ke kara kamari  da kuma yadda ake ci gaba da yi musu kisan gilla a kasar.

A nasa bangare Faustin-Archange Touadéra,shugaban kasar Afirka ta tsakiyan ya yi alawadai da yadda rikici ke kara kamari a kasar, inda ya tabbatar da cewa daga shekarar 2016 zuwa yanzu rikicin ya kara kamari.

A nasu bangare mahalarta zanga-zangar sunce a yayin yakin neman zabe shugaba Touadéra ya yi musu alkawarin cewa ba zai bari a cutar da musulmi ko guda a kasar ba.to yanzu ga sakamakon da suka gani.

Har ila yau mahalarta zanga-zangar sun ce idan aka ci gaba da irin tashin hankali a kasar to shakka babu ba za su iya gaba da rayuwa a kasar ba.

Tags

Apr 12, 2018 11:16 UTC
Ra'ayi