Apr 17, 2018 05:03 UTC
  • 'Yan Sanda Sun Kama Masu Zanga-Zangar Sako Sheikh Zakzaky 115

Rundunar 'yan sandan babban birnin tarayyar Nijeriya, Abuja, sun sanar da cewa suna tsare da 'yan kungiyar harkar Musulunci a Nijeriya (IMN) su 115 sakamakon dirar mikiyar da suka yi musu jiya Litinin da nufin tarwatsa jerin gwanon da suke ci gaba da yi a birnin Abujan don bukatar a sako musu shugabansu Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da gwamnatin take ci gaba da tsare shi.

Kafar watsa labaran Premium Times ta jiyo kakakin rundunar 'yan sandan Abujan, Anjuguri Manzah yana fadin cewa 'yan sandan sun kama 'yan kungiyar IMN din 115 a lokacin da 'yan sandan suke kokarin tarwatsa su, yana mai cewa ana ci gaba da gudanar da bincike kan hakikanin abin da ya faru, sannan kuma bayan an gama binciken za a gurfanar da mutanen a gaban kotu.

A jiya Litinin ne dai 'yan sandan suka yi amfani da karfin gaske wajen tarwatsa jerin gwanon da magoya bayan Harkar Musulunci da wasu masu rajin kare hakkin bil adama suke gudanarwa a Abujan domin  kira da a saki Sheikh Ibrahim Zakzaky, inda wasu bayanan suka ce mutum guda ya rasa ransa kana wasu da dama kuma sun sami raunuka.

An watsa hotuna na kyamara da kuma na bidiyo a shafukan watsa labarai na zamani da ke nuni da irin yadda 'yan sandan suka yi amfani da harsasai masu rai bugu da kari kan barkonon tsohuwa da tafasasshen ruwa wajen tarwatsa masu jerin gwanon, lamarin da ya sanya wasu cibiyoyi a Nijeriyan kiran da aka gudanar da bincike kan irin wannan amfani da karfi da 'yan sandan suka yi.

 

Tags

Ra'ayi