Apr 24, 2018 19:14 UTC
  • Habasha Ta Bukaci Birtaniya da Ta Mayar Mata Da Kayan Tarihinta Da Ta Wawushe

Jami'an gwamnatin kasar Habasha sun bukaci Birtaniya da ta mayarwa kasarsu kayan tarihi da ta wawushe tun a llokacin mulkin mallaka, da aka saka su a gidan tarihi na Virctoria and Albert da ke London.

Kamfanin dilalncin labaran Reuters ya habarta cewa, wannan kira dai ya zo baje wasu daga cikin kayan tarihi na kasar Habasha ta sojojin Birtaniya suka wawushe a lokacin mulkin mallaka, a lokacin da turawan Birtaniya suka kai wa Habasha hari a shekarar 1868.

Rahoton ya ce an saka wadannan kayan tarihi ne a babban wurin ajiye kayan tarihin nan na Victoria and Albert da ke birnin London, daga cikin kayan har da littafi kimanin 300, da kuma wasu kayayyakin da aka yi da hannu, da suka hada da mutum-mutumi da wasu kayayyaki da aka yi da zinariya tun fiye da shekaru 150 da suka gabata.

Ra'ayi