Apr 24, 2018 19:15 UTC
  • An Kashe Wani Matashi A zanga-Zangar Da Ake Yi A Afirka Ta Kudu

Jami'an 'yan sanda a kasar Afirka ta kudu sun sanar kashe wani matashi a zanga-zangar da ake yi a wasu yankunan kasar, domin nuna rashin amincewa da barna da dukiyar kasa.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, matashin dan shekaru 16 da haihuwa ya rasa ransa ne a wata gagarumar zanga-zangar da aka yi a daren jiya ne a garin Taung da ke arewa maso yammacin kasar ta Afirka ta kudu.

Masu zanga-zangar dai suna bukatar ganin an dauki matakan gaggawa wajen kakakbe dukkanin wadanda suke da hannu a cikin duk wani aiki na barna da dukiyar kasa ko cin hanci da rashawa, wadanda suke a cikin gwamnati ana damawa da su a halin yanzu, musamman ganin cewa gwamnatin Ramaphosa ta zo ne da sunan yaki da cin hanci da rashawa, amma kuma suna zargin cewa ana aiwatar da yaki da cin hancin ne kawai akan wadanda ba a dasawa da su.

A ranar Juma'a da ta gabata ce Ramaphosa ya bar taron kasashen renon Ingila a birnin Landan ba shiri, inda ya koma gida domin fuskantar wanann kalubale da ke a gabansa.

Tags

Ra'ayi