Apr 28, 2018 06:26 UTC
  • Harin Boko Haram Ya Hallaka Mutane 4 A Arewa Maso Gabashin Najeriya

Hukumar 'yansandar jahar Borno ta sanar da mutuwar mutum 4 a wani hari da mayakan boko haram suka kai birnin Maiduguri.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto hukumar 'yansandar jahar Borno a jiya juma'a na cewa an samu hasarar rayuka na mutum 4 da kuma jikkatar wasu 7 na daban a yayin da maharan kungiyar ta'addancin na Boko haram suka kai hari barikin soja na Giwa Barracks, inda ake tsare  da wasu Kwamanbdodinsu a Maiduguri babban birnin jahar.

Sanarwar ta ce sojojin dake cikin barikin tare da taimakon wasu jami'an tsaron da suka kai dauki da kuma taimakon sojojin  saman kasar sun samu nasarar murkushe harin.

A cikin 'yan kwanakin nan mayakan boko haram, sun tsananta kai hare-hare kan fararen hula da jami'an tsaron a arewa maso gabashin Najeriya, inda ko a ranar 5 ga wannan wata na Avrilu da muke ciki kimanin jami'an tsaron Najeriya 22 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu 75 na daban suka jikkata a yayin wani gumurzu da mayakan boko haram din a jahar ta Borno dake shiyar arewa maso gabashin kasar.

Tags

Ra'ayi