Mayu 03, 2018 05:23 UTC
  • IS Ta Dauki Alhakin Kai Harin Ofishin Hukumar Zabe A Libiya

Kungiyar 'yan ta'adda ta (IS) ta dauki alhakin kai harin kunan bakin wake da ta ce ya yi sanadin mutuwar mutum a kalla 15 a babban ofishin hukumar zabe na Tripoli.

Shafin yada farfagandan kungiyar na Amaq, ya wallafa a shafin twitter cewa an kai harin ne bisa umarnin kakakin kungiyar, Abu Hassan al-Moujahir. 

Sanarwar ta kara da cewa 'yan kunar bakin waken biyu, Abu Ayyub da Abu Tawfik, sun yi biyaya ne ga umurnin kakakin kungiyar inda suka kaddamar da hari kan ofishin zabe na makiya da masu goya masu baya. 

Wannan harin dai na suwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Libiyar dake samun goyan bayan MDD, hadin gwiwa da tawagar MDD ta (MANUL), a Libiya ke shirin shirya manyan zabuka a kasar ta Libiya kafin nan da karshen shekara nan.

Mataimakin hukumar zaben kasar, Abdalhakim Belkhaïr, ya shaida wa kamfanin diulancin labaren Sin na Xinhua cewa, wannan harin, manuniya ce hana gudanar da zabukan kasar dake tafe ta ko wanne irin hali. 

Tags

Ra'ayi