Mayu 20, 2018 12:18 UTC
  • Gwamnatin Libiya Da Ke Tabruk Ta Nuna Rashin Amincewarta Da Shawarar Kasar Faransa

Kakakin Majalisar Dokokin Libiya da ke da matsuguni a garin Tabruk ya bayyana rashin amincewarsu da shawarar da kasar Faransa ta gabatar a matsayin hanyar warware dambaruwar siyasar kasar.

Kakakin Majalisar Dokokin Libiya da ke da matsuguni a garin Tabruk Abdullahi Balhiq ya bayyana cewar al'ummar Libiya ce kadai take da hakkin samar da hanyar warware dambaruwar siyasar kasarta ba tare da tsoma bakin wata kasa ba.

Har ila yau Abdullahi Balhiq ya kara da cewa: Tuni Majalisar Dokokin Libiya ta amince da watan Satumba mai zuwa a matsayin lokacin gudanar da zaben shugaban kasa.

A halin yanzu haka dai Kasar Libiya tana da gwamnatoci biyu ne, daya a birnin Tripoli kuma kungiyoyin kasa da kasa suka amince da ita, yayin da ta biyu ke da matsuguni a garin Tabruk.

Tags

Ra'ayi