Mayu 23, 2018 17:35 UTC
  • Gwamnatin Angola Ta Kori Jami'an Diplomasiyyanta Biyu Saboda Batun Halartar Bude Ofishin Jakadancin Amurka A Qudus

Ministan harkokin wajen kasar Angola, Manuel Augusto, ya sallami babban daraktan harkokin Afirka, Gabas ta tsakiya da kungiyoyin kasashen yankin a ma'aikatar harkokin wajen Joaquim do Espírito Santo da kuma mukaddashin jakadan Angolan a ofishin jakadancin kasar a HKI, João Diogo Fortunato saboda halartar bikin bude ofishin jakadancin Amurka a birnin Qudus da mukaddashin jakadan yayi.

Rahotanni daga kasar Angolan sun ce ministan harkokin wajen Manuel Augusto ya sanar da wannan matakin ne cikin wasu sanarwa mabambanta da ya fitar inda ya ce ya dauki wannan matakin na korar jami'an biyu ne saboda gazawar da suka yi wajen kiyaye tsarin da gwamnatin ta tafi a kai, wanda hakan yana a matsayin wani kokari na bata sunan kyakkyawar sunan kasar Angolan a idon duniya.

Jaridar gwamnatin kasar Angolan ta ce mukaddashin jakadan Angolan João Diogo Fortunato ya halarci bikin bude ofishin jakadancin Amurka a birnin Qudus ne bisa amincewar Joaquim do Espírito Santo a matsayinsa na  babban daraktan harkokin Afirka, Gabas ta tsakiya da kungiyoyin kasashen yankin a ma'aikatar harkokin wajen wanda hakan ya saba wa matsayar gwamnatin Angolan.

A kwanakin bayan ne dai Amurkan ta bude ofishin jakadancinta a birnin Qudus wacce shugaban kasar Donald Trump ya bayyana a matsayin babban birnin HKI lamarin da yake ci gaba da fuskantar tofin Allah tsine a duk fadin duniya. Kasashe 86 ne dai aka gayyace su bikin sai dai da damansu sun ki halarta don nuna rashin amincewarsu da wannan mataki da Amurkan ta dauka.

Tags

Ra'ayi