Jun 03, 2018 12:07 UTC
  • An Gudanar Da Zanga Zangar Yin Allah Wadai Da Canza Kundin Tsarin Mulkin A Kasar Komoro

Jam'iyyun Adawa a kasar Komorro sun gudanar da zanga zangar yin Allah wadai da shirin gwamnatin kasar na gudanar da zaben raba gardama don gabatar da sauye sauye a cikin kundin tsarin mulkin kasar.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayyana cewa a jiya Asabar ne jam'iyyun adawar kasar suka gudanar da zanga zanga a duk fadin kasar ta Komoro don nuna rashin amincewarsu da duk wani kokari na sauyi a cikin kundin tsarin mulkin kasar.

Kafin haka dai shugaban kasar ta Komoro Gazali Usmani ya bukaci kotun kundin tsarin mulkin kasar ta fara shirye shiryen gudanar da zaben raba gardama don ba shi damar aiwatar da sauye sauye a cikin kundin tsarin mulkin kasar  a karshen wannan watan.. 

A ranar Jumma'a da ta gabata ma, magoya bayan jam'iyun adawar kasar sun kara da jami'an tsaro bayan sallar jumma'a a masallacin Alkasimi da ke babban birnin kasar Muruni . A ranar 29 ga watan Yuni da muke ciki ne dai ake saran za'a gudanar da zaben raba gardaman 

Tags

Ra'ayi