Jun 09, 2018 10:42 UTC
  • Gwamnatin Tarayyar Nijeriya Ta Mayar Da Martani Ga Kalaman Obasanjo

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta mayar da martani ga ikirarin tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo na cewa gwamnatin tana kokarin kitsa makarkashiyar kama shi, tana mai cewa mara gaskiya ne kawai zai ji tsoron shari'a.

Ministan watsa labarai da ala'adu na Nijeriya din Alhaji  Lai Mohammed ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar inda ya ce babban abin da gwamnatin Muhammadu Buhari ta sa a gaba shi ne gyara irin barnar da aka yi a kasar na shekaru 16 don haka ba ta ma da lokacin kitsa wata makarkashiya ga wani.

Alhaji Mohammed ya ci gaba da cewa marasa gaskiya ne kawai za su ji tsoron duk wani bincike da za a gudanar, yana mai cewa shugaba Buhari da gwamatinsa sun kuduri aniyar kare dukkanin 'yan Nijeriya daga duk wata barazana da za ta iya fuskantarsu, kawai dai marasa gaskiya su ne za su ji tsoron gwamnatin wacce ta kuduri aniyar fada da duk wani rashin gaskiya da cin amana.

A jiya Juma'a ne tsohon shugaban Nijeriya Cif Olesegun Obansanjo yayi zargin cewa cewa shugaba Buhari na ci gaba da tattara shaidu na boge da nufin kama shi sakamakon sukar gwamantinsa da yake yi.

 

Tags

Ra'ayi