Jun 11, 2018 17:02 UTC
  • Nijeriya Da Moroko Sun Sanya Hannu Kan Wasu Yarjejeniyoyi Na Kasuwanci

Gwamnatocin Nijeriya da Moroko sun sanya hannu kan wasu yarjejeniyoyi guda uku da suka hada batun bututun shimfida bututun iskar gas da zai ba wa Nijeriya damar isar da iskar gas zuwa kasashen Yammacin Afirka har zuwa kasar Moroko da kuma Turai.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ce an sanya hannu kan yarejeniyoyin ne a yau din nan Litinin a birnin Rabat, babban birnin kasar Morokon a gaban shugaban Nijeriya din Muhammadu Buhari  da kuma sarkin Moroko Muhammadu na 6 bayan ganawar da ta hada shugabannin biyu a ci gaba da ziyarar aiki ta kwanaki biyu da shugaba Buharin ya ke yi a kasar Morokon.

A bisa yarjejeniyar dai an tsara cewa za a fara aikin shimfida bututun iskar gas din wanda zai kai tsawon kilomita 5600 a mataki-mataki gwargwadon bukatar da ake da shi har zuwa kasashen Turai cikin shekaru 25, sannan hakan kuma zai ba wa Nijeriya din sayar da iskar gas din da take da shi da kuma karfafa tattalin arzikin kasar.

Baya ga yarjejeniyar iskar gas din har ila yau kuma kasashen biyu sun sanya hannu kan wata yarjejeniya ta ayyukan gona da musayen kwarewar da ake da ita a wannan bangaren tsakanin kasashen biyu wadanda ministocin ayyukan gona na kasashen biyu Audu Ogbeh da Aziz Akhannouch suka sanya wa hannu.

A jiya Lahadi ne dai shugaba Buharin ya fara ziyarar aiki ta kwanaki biyu a kasar Morokon bisa gayyatar da sarkin kasar yayi masa.

Tags

Ra'ayi