Jun 13, 2018 15:14 UTC
  • AU Na Maraba Da Bukatar Sudan Ta Karbar Bakuncin Taron Sulhun Sudan Ta Kudu

Tarayyar Afrika AU, ta yi maraba da bukatar da Sudan ta gabatar, ta neman karbar bakuncin taro tsakanin shugaban Sudan ta Kudu Salva Kirr da shugaban 'yan adawa na kasar Reik Machar.

Ana sa ran taron zai farfado da shirin wanzar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu, tare da bukatar bangarori dake adawa da juna, su aiwatar da yarjejeniyar da IGAD ta cimma a watan Agustan shekarar 2015.

A cewar Wakil Amutingon, mukaddashin shugaban ofishin AU mai shiga tsakani dake Khartoum, AU na maraba da duk wani mataki da zai iya kai wa ga cimma zaman lafiya a Sudan ta Kudu.

A watan Mayun da ya gabata ne, ministocin harkokin wajen kasashe mambobin kungiyar raya yankin gabashin Afrika IGAD, suka amince da gudanar da wani taron gaba da gaba, tsakanin shugaba Kirr da Riek Machar.

Tun a watan Disamban shekarar 2013 kasar Sudan ta Kudu ta tsunduma yakin basasa, al'amarin da ya yi sanadin mutuwar mutane kimanin 10,000 tare da raba wasu miliyoyi da matsugunansu.

Tags

Ra'ayi