Jun 16, 2018 19:03 UTC
  • Harin Ta'addanci Ya Ci Rayukan Mutum 3 A Arewacin Kamaru

'Yan Boko Haram sun kai harin kunar bakin wake a kusa da wata makarantar gwamnati a yankin Limani na arewacin kasar Kamaru.

Kamfanin dillancin labaran Xin huwa na kasar Sin ya habarta cewa 'yan ta'addar boko haram biyu da wani farar hula guda sun hallaka sanadiyar harin kunar bakin wake da 'yan boko haram din suka kai a garin Maura na yankin Limani na arewacin kasar Kamaru, sannan wani dan kunar bakin waken guda ya gudu.

Wannan hari na kunar bakin wake na zuwa ne kwana guda da aka kashe wasu 'yan kunar bakin wake da suka yi kokarin kai hari a yayin da ake bukukuwan karamar salla a yankin.

A ranar 8 ga watan yunin da muke ciki, kimanin fararen hula 10 da 'yan ta'addar boko haram 4 ne suka hallaka sanadiyar harin ta'addancin da aka kai yankin Manga-Jalingo dake arewacin kasar.

Tags

Ra'ayi