Jun 17, 2018 12:08 UTC
  • Kamaru: An kashe Mutane 3 A Harin Ta'addanci

Kamfanin dillancin labarun Xinhua na kasar sin ya ambato majiyar tsaron kasar Kamaru na cewa mutane 3 sun mutu ne sanadiyyar harin kunar bakin wake da aka kai a yankin Limani da ke arewacin kasar ta kamaru

Harin na yau ya zo ne bayan wani kwatankwacinsa da wasu 'yan kungiyar Boko haram su ka kai a lokacin da ake bikin karamar salla.

A ranar 8 ga watan nan na Yuni an kashe fararen hula 10 da kuma 'yan ta'addar kungiyar ta boko haram a yankin Mangawe-Jalingo da ake arewacin kasar ta Kamaru.

Daga shekarar 2009 zuwa yanzu kungiyar Boko Haram ta kashe mutane fiye da 20,000 a cikin kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi.

 

Tags

Ra'ayi