• Yan Adawa A Mauritaniya Zasu Hada Kai Domin Kawo Karshen Gwamnatin Kasar

Jam'iyyun adawa akalla 10 ne suka bayyana shirinsu na hada kai domin tunkarar zabukan 'yan Majalisun Dokokin Mauritaniya da nufin kawo karshen gwamnatin kasar.

A taron manema labarai da ya gudanar: Jagoran gamayyar jam'iyyun adawar Mauritaniya Muhammad Wuld Maulud ya bayyana cewa: A halin yanzu haka akwai jam'iyyun adawar kasar akalla 10 da suka bayyana shirinsu na hada kai domin tunkarar zabukan 'yan Majalisun Dokokin kasar da na kananan hukumomi da za a gudanar a watan Satumban wannan shekara da nufin kawo karshen gwamnatin kasar karkashin shugabancin Muhammad Wuld Abdul-Azizi.

Maulud ya kara da cewa: Mahukuntan Mauritaniya suna shirya duk wata makarkashiyar ganin sun rusa gamayyar jam'iyyun adawar kasar da zata iya kawo musu cikas a zabuka amma hakarsu bata kai ga ruwa ba.

A shekara ta 2013 dai gamayyar jam'iyyun adawar Mauritaniya sun haramta zabukan 'yan Majalisun Dokokin kasar da na kananan hukumomi lamarin da ya bai shugaban kasar Muhammad Wuld Abdul-Aziz da jam'iyyun da suka mara masa baya gagarumar rinjaye a Majalisun kasar.

Tags

Jun 24, 2018 06:49 UTC
Ra'ayi