Jun 24, 2018 12:49 UTC
  • Rikicin Kabilanci Ya Ci Rayukan Mutane 27 A Kasar Habasha

Kamfanin dillancin labarun Xinhua ya ambato shugaban 'yan sanda a yankin Fissheha Garedewe ne ya sanar da cewa an yi fada a tsakanin kabilun Sidama da Wolaita.

Sanarwar ta ce baya ga mutane 27 da aka kashe, an jikkata wasu fiye da 600,000.

Garedewa ya kara da cewa; Tuni an kame mutanen da  suke da hannu a cikin rikicin, sannan kuma ya yi ga mutane da su ba su hadin kai a ci gaba da bincken da suke yi.

A farkon watan Yuni ma an yi  wata taho mu gamar a tsakanin wadannan kabilun biyu a garin Awasa inda ya ci rayukan mutane 10.

Sidama da Wolaita su na cikin manyan kabilu a kudancin kasar, sai dai alaka a tsakaninsu ba ta da kyau.

Tags

Ra'ayi