• Matsalar Tsaro Na Iya Yin Tasiri Wajen Haifar Da Matsalar Abinci A Yankin Sahel

Ministocin noma na kasashen yankin Sahel sun yi gargadin cewa matsalolin tsaro da ake fuskanta kan iya yin babban tasiri wajen haifar da matsalolin abinci a kasashen yankin.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya habarta cewa, a taron da ministocin noma na kasashen yankin Sahel suka gudanar a birnin Yamai na jamhuriyar Nijar, sun jaddada wajabcin kara mayar da hankali kan batun, domin rashin tsaro shi ne zai iya kawo babban cikas ga harkokin noma da samar da abinci a yankin.

Haka nan kuma ministocin noman kasashen yankin sahel sun nuna damuwa kan matsalolin da ake samu a yankin tafkin Chadi da sauran yankuna da suka hada Mali da Burkina Faso da Nijar, wanda hakan ya yi tasiri ga rakokin noma da samar da cimaka matuka.

 

Tags

Jul 10, 2018 17:19 UTC
Ra'ayi