Jul 11, 2018 07:01 UTC
  • Gwamnatin Kasar Tunisia Ta Ce Yaki Da Ayyukan Ta'addanci A Kasar Zai Dauki Lokaci

Friministan kasar Tunisia ya bayyana cewa gwamnatinsa zata dau fansa kan kissan da yan ta'adda suka yiwa jami'an tsaron kasar masu tsaron kan iyakokin kasar a kwanakin da suka gabata.

Kamfanin dillancin labaran Spotnic ya nakalto Yusuf Shahida Priministan kasar Tunisia yana fadar haka ya kuma kara da cewa yaki da ayyukan ta'addanci a kasar zai dauki lokaci, kuma kasar Tunisia ya zuwa yanzu ta sami nasarorim masu yawa a kan kungiyoyin yan ta'adda a kasar. 

Friministan ya kara da cewa manufar yan ta'adda na kai hare hare kan jami'an tsaron kan iyakar kasar a cikin kwanakin da suka gabata ita ce yin watsi da irin ci gaban da gwamnatin kasar ta samu a fagen tattalin arziki da kuma hakkin mata da yencin da muatanen kasar suke ciki.

A jiya ne majalisar koli ta tsaron kasar Tunisia ta kira taron koli na tsaron kasar wanda ya sami halattar  shugaban kasar Albaji Qaed Assibsi, friministan kasar, ministan tsaro da kuma alkalin alkalan kasar .

A ranar asabar da ta gabata ce yan ta'adda suka tada bom wanda ya tarwatsa jirgin ruwan da ke dauke da jami'an tsaron kan iyakar kasar a garin Gharuddimaa na jihar Jundubeh kusa da kan iyakar kasar da kasar Algeria, inda jami'an tsaro 8 suka rasa rayukansu. 

Tags

Ra'ayi