Jul 11, 2018 07:05 UTC
  • Wani jirgin Fasinja Ya fadi A Kasar Afrika Ta Kudu

Faduwar wani jirgin sama a kasar Afrika ta kudu ya yi sanadiyyar mutuwar mutun akalla guda sannan wasu 20 suka ji rauni.

kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto hukumar bada agajin gaggawa ta kasar Afrika ta kudu tana fadar haka , ta kuma kara da cewa jirgin saman ya fadi ne a jiya talata kusa da tashar jiragen sama na Wonderboom a cikin birnin Protoria babban birnin kasar.

Akwai yiyuwan yawan wadanda suka rasu rayukansu ya karu don wasu daga cikin wadanda suka ji rauni suna cikin mummunan hali. 

Wadanda suka ganewa idanunsa faduwar jirgin sun bayyana cewa kafin faduwar jirgin, injinsa ya kama da wuta. Majiyar gwamnatin kasar ta bayyana cewa za'a fara gudanar da bicnike don gano musabbin faduwar jirgin. 

 

 

 

 

Ra'ayi