• Sudan Ta Kudu:

Kakakin 'yan tawayen na Sudan ta kudu Lam Paul Gabriel ya ce; sojojin gwamnati 200 sun kai wa yan tawayen hari wanda hakan keta yarjejeniyar tsagaita wuta ce

Gabriel ya yi suka da kakkausar murya ga ziyarar da babban hafsan hafsoshin sojan kasar ya yi zuwa sin yana mai cewa; Manufar ziyarar ita ce sayen makamai wanda shi ma ya sabawa yarjejeniyar tsagaita wuta da bangarorin biyu su ka cimmawa.

An yi yarjejeniyar tsagaita wuta a tsakanin shugaban kasa Salva Kiir da kuma tsohon mataimakinsa Riek Machar a ranar 28 ga watan Yuni a kasar sudan. Shugabannin kasashen Sudan Umar Hassan al-Bashir da kuma na Uganda Yuweri Musaveni sun halarci rattaba hannu akan yarjejeniyar.

A ranar juma'ar da ta gabata ma dai bangarorin biyu sun cimma wata yarjejeniyar ta fitar da makamai daga cikin birane.

 

Tags

Jul 12, 2018 06:38 UTC
Ra'ayi