Jul 15, 2018 19:16 UTC
  • Sojojin Nigeriya 23 Sun Bace Babu Labarinsu Bayan Sun Fuskanci Harin Kungiyar Boko Haram

Wata majiyar sojin Nigeriya ta sanar da cewa: Sojojin kasar 23 ne suka bace babu labarinsu bayan da suka fuskanci harin mayakan kungiyar ta'addanci ta Boko Haram a garin Bama da ke jihar Borno a shiyar arewa maso gabashin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya habarta cewa: Wani jami'in sojin Nigeriya da ya bukaci a sakaye sunansa ya bayyana cewa: A yammacin ranar Juma'ar da ta gabata sun samu labarin cewar wasu gungun mayakan kungiyar Boko Haram kimanin 100 sun taru a yankin Boboshe da ke kauyen Balagallaye da ke garin Bama a jihar Bornon Nigeriya, don haka sojojin gwamnatin kasar suka sabi makamai da nufin kai farmaki kan 'yan ta'addan, inda mayakan kungiyar ta Boko Haram suka musu kofar rago, a cikin motoci goma sha daya, uku ne kacal suka sha da kyar.

Majiyar ta kara da cewa har yanzu babu labarin sojoji 23 da suka hada da manyan jami'ai 5 da kananan sojoji 18, kodai sun mutu ko an kama su a matsayin fursunonin yaki ko kuma sun bazama daji domin tsira da rayuwarsu.

Tags

Ra'ayi