Aug 05, 2018 12:36 UTC
  • Shugaban Kasar Comoro Ya Yi Alkawalin Gudanar Da Manyan Zabuka Anan Gaba

Shugaban Kasar Gazali Usman ya fada a yau Lahadi cewa; Idan aka sami kyakkyawan yanayi to za a gudanar da manyan zabuka a kasar

Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ambato shugaban kasar yana cewa; Kasar tana fuskantar karancin baje koli wanda zai kawo cikas a harkar zabe.

A cikin kwanakin bayan nan ne dai al'ummar kasar ta Comoro su ka kada kuri'ar raba gardama akan sabon tsarin mulkin kasar wanda ya bai wa shugaban kasa damar yin tazarce.

Sai dai 'yan hamayyar siyasar kasar suna nuna rashin amincewarsu da kada kuri'ar kuma sun kaurace masa.

Tags

Ra'ayi