Aug 11, 2018 19:20 UTC
  • Aljeriya Ta Yi Kakkausar Suka Kan Kisan kiyashin Da Isra'ila Ta Ke Yi Kan Falastinawa

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Aljeriya ya bayyana hare-haren da Isra'ila take kaddamarwa kan yankin zirin Gaza da cewa ayyukan yaki ne a kan fararen hula marassa kariya.

Kamfanin dillancin labaran IRNA ya habarta cewa, Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Aljeriya Abdulaziz bin Ali Al-sharif ya bayyana cewa, kasarsa ba za ta taba yin kasa a gwiwa ba wajen nuna cikakken goyon bayanta ga al'ummar Palastine.

Haka na kuma ya kirayi dukkanin al'ummomin duniya da su sauke nauyin da ya rataya  akansu, domin ganin an kawo karshen zubar da jinin Dalastinawa da kisan kiyashin da Isra'ila ke yi a kansu a kullum rana ta Allah.

Tun daga ranar 30 ga watan Maris da ya gabata ya zuwa yanzu, Isra'la ta kashe Falastinawa 161, tare da jikkata wasu dubbai da kuam kame wasu.

Tags

Ra'ayi