Aug 13, 2018 19:12 UTC
  • Prof. Osinbajo Zai Kasance Mataimakin Shugaban Buhari A Zaben Shekara Ta 2019

Mukaddashin shugaban kasar Najeria farfesa Yemi Osingbaji zai ci gaba da kasancewa mataimakin shugaba Buhari a zaben shekara ta 2019

Jaridar Punch ta Najeriya ta nakalto mai bawa shugaban kasa shawara kan lamuran watsa labarai Malam Shehu garba ya fadawa yan jiridu a fadar shugaban kasa  a yau litinin.

Shehu garba ya kara da cewa irin nasararorin da jam'iyyar APC ta samu a zabubbukan da aka gudanar a wasu jihohi a cikin yan kwanakin da suka gabata sun nuna cewa jam'iyyar zata lashe zaben shugaban kasa a shekara mai zuwa.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya bayyana cewa jam'iyyar APC ce ta lashe zabubbukan cike gurbi na sanatoci a jihohin katsina Bachi da kuma na majalisar wakilai a jihar Kogi wadanda aka gudanar a cikin yan kwanakin da suka gabata .

 

Tags

Ra'ayi