Aug 14, 2018 13:23 UTC
  • Harin Kunar Bakin Wake Ya Hallaka Mutum 10 A Najeriya

Wasu mutane biyu da ake zaton mayakan boko haram ne sun kai harin kunar bakin wake a jahar Adamawa dake shiyar arewa maso gabashin Najeriya

Kamfanin dillancin labaran Meher ya nakalto hukumar 'yan sandar Najeriya na cewa maharar suka kai harin kunar bakin waken ne tare da garin Madagali dake jahar Adamawa, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar Mutum 10 da kuma jikkata wani adadi mai yawa.

Sanarwar ta hukumar 'yan sandar Najeriyan ta ce a halin yanzu ba za su iya bayyana adadin mutanan da suka jikkata ba sanadiyar wannan hari, kuma akwai yiyuwar adadin wadanda suka rasa rayukansu ya karu, ganin mawuyacin halin da wasu daga cikin wadanda suka jikkatar ke ciki.

Tun a shekarar 2009,kungiyar boko haram ta fara kai hare-hare a arewacin Najeriya, sannan a shekarar 2015, kungiyar ta fadada kai hare-haren a kasashen Kamaru, Tchadi da Nijer, lamarin da ya yi sanadiyar salwantar rayukan mutune sama da dubu 20 yayin da ya raba wasu sama da miliyan biyu da dubu 600 da mahalinsu.

Tags

Ra'ayi