Aug 14, 2018 13:23 UTC
  • An Hallaka 'Yan Ta'adda 14 A Gabashin Libiya

Sojojin kasar Libiya sun sanar da hallaka 'yan ta'adda 14 a gabashin kasar

Hukumar gidan Radio da Talabijin din kasar Iran ta nakalto Rundunar tsaron kasar Libiya karkashin jagorancin Janar Khalifa Haftar cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Litinin sojojin kasar sun fafata da 'yan ta'adda a wani yanki dake iyaka da gariruwan Tobruk da Ajdabiya na gabashin kasar tare da kame wasu da kuma hallaka 14 daga cikinsu.

Sanarwar ta ce wadanda ake kame 'yan ta'addar da suka gudu ne daga garin Derna, kafin hakan dai garin Derna na karkashin mamayar Majalisar Shura ta mujahideen mai alaka da kungiyar alQa'ida.

Tun a shekarar 2011 ne kasar Libiya ta fada cikin rikici bayan juyin milkin da 'yan tawaye bisa goyon bayan Amurka da kungiyar tsaron Nato suka yi wa marigayi kanal Mu'amar Kaddafi, lamarin da ya sanya 'yan ta'adda daga sassa daban daban na Duniya suka kafa sansaninsu a kasar.

Tags

Ra'ayi