Aug 15, 2018 19:08 UTC
  • Yansanda A Jihar Zamfara Sun Kama Yan Bindiga 20 Tare Da Bindigogi 7

Yansanda a jihar Zamfara na tarayyar Najeriya sun bada labarin kama yan bindiga 20 da kuma bindogogi 7 a wurare daban daban a jihar.

Jaridar Daily Trusta ta Najeriyan ta nakalto kwamishinan yansanda na jihar ta Zamfara Mr Kenneth Ebrimson yana fadar haka a Gusaiu babban birnin Jihar. Ya kuma kara da cewa sun sami nasarar capke yan bindigan ne tare da taimakon jami'an yansandan ciki, wadanda suke dade suna bin sawunsu. 

Kwamishinan ya nuna bindigogin da aka kama a hannunsu, amma ya ce ba'a zo da su ba, kuma ba zai bayyana sunayensu ba don an fara yi masu tambayayi, don haka zuwa da su ko fadar sunayensu yana iya shafar binciken da ake masu.

Daga karshe kwamishinan ya kammala da rokon mutane su taimakawa jami'an tsaro tare da duk wani labari da suke da shi don gani mabuyar yan bindiga da da suka dade suka kashe mutanen jihar 

 

 

Tags

Ra'ayi