Aug 19, 2018 12:28 UTC
  • Shugaba Buhari Ya Yi Alkawarin Daure Barayi Da Dama

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya sha alwashin kamawa tare da hukunta karin manyan jami’ai da ‘yan siyasar da suka jefa tattalin arzikin kasar cikin mummunan hali ta hanyar wawashe kudaden al’umma.

Shugaba Buhari wanda ya koma gida da yammacin jiya Asabar, bayan ya kare hutun kwanaki goma a birnin London ya yi wannan bayani ne yayin ganawa da manema labarai a filin jragen sama na Abuja, kafin isa fadar gwamnati.

Shugaban ya ce ‘yan Najeriya suna yi masa kyakkyawan zaton zai tabbatar da an hukunta wadanda suka yi sama da fadi da dukiyoyinsu, kuma tabbas ba zai watsa musu kasa a ido ba, domin ba shakka hukunta wadanda suka yi wadaka da kudaden al'umma ya zama tilas.

A ranar 3 ga watan Agusta, 2018, shugaba Buhari ya fara hutun kwanaki 10 a birnin London, inda mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo ya ci gaba da tafiyar da al’amuran kasar a matsayi mukaddashin shugaba.

Tags

Ra'ayi