Aug 20, 2018 06:41 UTC
  • Watannin 6 Kafin Zaben Shekara Ta 2019 Amma Akwai Katunan Zabe Miliyon 7.5 Wadanda Ba'a Karba Ba

Watannin 6 kafin a gudanar da zabubbuka a tarayyar Najeriya amma har yanzun mutane mutane kimani miliyon 7.5 ba je suka karbi katunansu na zabe a hukumar zaben kasar ba.

A wani bancike wanda jaridar Daily Trusta ta yi ya nuna cewa katunan zabe na din din din miliyon 7,458,291 ne masu su ba su zo sun karba ba. Rahoton ya kara da cewa Jihar Lagos ce a gaba tare da katunan zabe 1,380,142 wadanda ba'a karba ba.  

Rahoton ya bayyana cewa an sami ci gaba a wajen karbar katunan zaben idan an kwatanta da shekarun baya. A cikin watanni 3 na farlkon wannan shekara an karbi katunan zabe 121,097, sai kuma watanni ukku na biyu kuma aka karbi katuna 461,838 wanda ya nuna jimillan katunan da aka karba a cikin watanni 6 sun kai 813,110. 

Mr Rotimi Lawrence Oyekanmi, jami'in watsa labarai na shugaban hukumar Zabe Prof. Mahmood Yakubu ya ce duk wanda zai karbi katin zabe na din din din dole ne sai ya gabatar da katin wucin gadi da aka bashi a lokacin rigista. 

Hukumar zaben ta Nigeria INEC ta bayyana cewa sabbin rigistan karban katin zaben ya zuwa 15 ga watan Augusta da muke ciki ya kai 12,682,792.

 

Tags

Ra'ayi