Aug 22, 2018 18:56 UTC
  • Kungiyar Hadin Kan Kasashen Larabawa Ta Bukaci A Ba Da Kariya Ga Masallacin Kudus

Kungiyar Hadin kan kasashen Larabawa ta yi kira ne ga MDD da ta kawo karshen keta hurumin masallacin Kudus da HKK take yi

Kamfanin dillancin labaran Anatoli na kasar Turkiya ya ambato  Saeed Abu Ali wanda shi ne mataimakin babban sakataren kungiyar ta kasashen larabawa yana yin wannan kiran a jiya talata.

Kiran ya zo ne adaidai lokacin da ake tunawa da lokacin da wani dan Shayoniya ya tashi gobara a cikin masallacin na kudus.

Mataimakin babban magatakardar kungiyar hadin kan kasashen larabawan ya ci gaba da cewa; Abin da haramtacciyar kasar Isra'ila take yi a yanzu shi ne kokarin sauya tarihi da kamannin masallacin na kudus.

 Saeed Abu Ali ya kuma yi suka akan yadda 'yan sahayoniyar suke kokarin tilasta wa Palasdinawa mazauna birnin Kudus barin gari domin su ci gaba da mamaye shi

 

Tags

Ra'ayi