Aug 26, 2018 19:05 UTC
  • Sabon Zababben Shugaban Kasar Zimbabwe Ya Yi Rantsuwar Kama Aiki

Sabon zababben shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya yi rantsuwar kama aiki tare da jaddada aniyarsa ta samar da sabuwar kasar Zimbabwe.

A jawabin da ya gabatar a babban filin wasanni na birnin Harare fadar mulkin kasar Zimbabwe bayan rantsar da shi a matsayin sabon shugaban kasar a yau Lahadi: Shugaba Emmerson Mnangagwa ya jaddada alkawarin da ya dauka a lokacin yakin neman zabe na gudanar da gyare-gyare a kasar musamman shawo kan matsalar tattalin arziki da Zimbabwe ta tsunduma ciki tsawon lokaci.

Mnangagwa ya bayyana cewa: Babban shirinsa a fagen farfado da harkar tattalin arzikin Zimbabwe shi ne janyo masu zuba hannun jari daga ciki da wajen kasar da samar da guraban ayyukan yi musamman a tsakanin matasa.

A ranar Juma'ar da ta gabata ce kotun kundin tsarin mulkin Zimbabwe ta sanar da halaccin zaben da aka yi wa Emmerson Mnangagwa bayan da ta yi watsi da dukkanin korafe-korafen da madugun 'yan adawar kasar Nelson Chamisa ya gabatar mata kan rashin ingancin zaben da aka gudanar a ranar 30 ga watan Yulin da ya gabata a kasar. 

Tags

Ra'ayi