Aug 27, 2018 12:25 UTC
  • Jam'iyyar ٍEnnahda Ta Tunusiya Ta Jaddada Sharuddinta Na Ci Gaba Da Goyon Bayan Gwamnatin Kasar

Shugaban Majalisar Shawara ta jam'iyyar Ennahda ta kasar Tunusiya ya jaddada cewa; Sharadin jam'iyyarsu na ci gaba da gudanar da aiki da fira ministan kasar shi ne dole ne a gudanar da garambawul a Majalisar Ministocin Kasar.

Shugaban Majalisar Shawara ta jam'iyyar Ennahda ta kasar Tunusiya Abdul-Karim al-Haruni ya bayyana cewa: Jam'iyyar Ennahda zata ci gaba da goyon bayan fira ministan kasar Yusuf al-Shahid domin ci gaba da jagorancin majalisar ministocin kasar ne matukar zai gudanar da garambawul a majalisar ministocin kasar.

Al-Haruni ya kara da cewa: Dole ne gwamnatin  Yusuf al-Shahid ta kara matsa kaimi a fagen yaki da ta'addanci da barnata dukiyar kasa.

 

Tags

Ra'ayi