• Fira Ministan Tunusiya Ya Kori Ministan Makamashin Kasar Kan Zargin Cin Hanci Da Rashawa

Fira ministan Tunusiya ya sallami ministan makamashin kasar tare da wasu manyan jami'ai hudu a ma'aikatar daga aiki kan zargin cin hanci da rashawa.

Kamfanin dillancin labaran Reuters a yau Juma'a ya watsa rahoton cewa: Fira ministan Tunisiya Yusuf Sha'hid ya kori ministan makamashin kasar Khaled Kaddour gami da manyan jami'ai hudu a ma'aikatar daga aiki bayan zargin samunsu da laifin cin hanci da rashawa.

Rahoton ya kara da cewa: Manyan jami'an da aka kora daga aikin sun hada da sakataren ma'aikatar makamashin kasar da babban diraktan harkar man fetur da kuma shugaban kamfanin kula da harkokin man fetur na kasar gami da babban dirakta mai kula da harkokin doka a ma'aikatar makamashin.

Kamar yadda fira ministan kasar ta Tunusiya ya nada kwamitin da zai gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake yi kan yin sama da fadi da dukiyar kasa a ma'aikatar makamashin kasar. 

Tags

Aug 31, 2018 12:58 UTC
Ra'ayi