Sep 01, 2018 19:08 UTC
  • An Kai Hari Ta Sama  Kan 'Yan Ta'adda A Yammacin Tunusiya

Ma'aikatar tsaron Tunusiya ta sanar da kai hari ta sama kan kungiyoyin 'yan ta'adda a tsibirin Magilah na jahar Kasrin dake yammacin kasar.

Hukumar radio da talabijin din kasar Iran ta  nakalto ma'aikatar tsaron Tununsiya a wannan asabar na cewa dakarun saman kasar sun kai hari cikin daren jiya juma'a a maboyar 'yan ta'adda dake tsaunukan Magilah na jahar Kasrin, tare da hallaka da dama daga cikinsu.

Saidai sanarwar ba ta yi karin haske ba kan adadin 'yan ta'addar da aka hallaka.

Tun a shekarar 2011 ne kasar Tunusiya ke fuskantar matsalar 'yan ta'adda, inda cikin wani rahoto da MDD ta fitar, sama da 'yan kasar Tunusiya dubu biyar ne ke sahun kungiyoyin 'yan ta'adda dake  kasashen Iraki da Siriya.

Kashin da 'yan ta'adda suka sha a kasashen siriya da Iraki shi ya sanya 'yan ta'adda suka watsu zuwa wasu kasashe irinsu Tunusiya da sauransu.

Tags

Ra'ayi