Sep 05, 2018 18:56 UTC
  • 'Yan Kungiyar Al-Shabab Ta Somaliya Sun Kashe Mutane Shida A Sassan Birnin Mogadishu

Rundunar 'yan sandan Somaliya ta sanar da cewa: Mayakan kungiyar ta'addanci ta Al-Shabab ta kasar sun kaddamar da harin wuce gona da iri a birnin Mogadishu fadar mulkin kasar da ya yi sanadiyyar mutuwar sojojin gwamnati hudu.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya habarto daga majiyar rundunar 'yan sandan Somaliya cewa: Wasu mayakan kungiyar ta'addanci ta Al-Shabab sun kaddamar da farmaki kan ayarin rundunar sojin kasar a kan hanyar birnin Mogadishu fadar mulkin kasar, inda suka kashe sojoji hudu nan take.

Har ila yau mayakan kungiyar ta Al-Shabab sun harbe wasu mutane biyu har lahira a birnin na Mogadishu, kuma maharan sun samu nasarar tserewa bayan kai harin.

A jiya Talata ma kungiyar Al-Shabab ta kai harin kunan bakin wake a birnin na Mogadishu fadar mulkin kasar ta Somaliya da yayi sanadiyyar mutuwar mutane shida uku daga cikinsu sojojin gwamnatin kasar tare da rushewar gine-ginen gwamnati da wata makaranta.  

Tags

Ra'ayi