Sep 05, 2018 19:01 UTC
  • Rikicin Kasar Libiya Na Baya-Bayan Nan Ya Lashe Rayukan Mutane Fiye Da Sittin

Dauki ba dadi tsakanin kungiyoyi masu dauke da makamai a birnin Tripoli fadar mulkin kasar Libiya a cikin mako guda kacal ya lashe rayukan mutane fiye da 60 tare da jikkata wasu 159 na daban.

Kakakin cibiyar kula da ayyukan jin kai a fannin kiwon lafiya a birnin Tripoli fadar mulkin kasar Libiya Isamah Ali ya bayyana cewa: Dauki ba dadi tsakanin kungiyoyin da suke dauke da makamai a birnin Tripoli fadar mulkin Libiya da kuma gefen kudancin birnin kasar a cikin mako guda kacal ya lashe rayukan mutane akalla 61 tare da jikkata wasu 159 na daban, baya ga tilastawa jama'a kimanin 1,825 tserewa daga muhallinsu.

A gefe guda kuma majiyoyin watsa labaran Libiya sun sanar da cewa: A cikin 'yan watannin nan an sace matan aure 11 da budurwaye 21 a yankuna daban daban na kasar ta Libiya. Kamar yadda Ma'aikatar harkokin cikin gidan Libiya ta fitar da rahoton cewa: A Shekara ta 2017 da ta gabata an samu rahotonnin sace mutane da yawansu ya kai 1,400 a sassa daban daban na kasar.  

Tags

Ra'ayi