Sep 07, 2018 19:04 UTC
  • Libya: Janar Haftar Ya Barazanar Cewa Sojoji Za Su Kwace Iko Da Birnin Tripoli

Bbaban hafsan hafsoshin sojin kasar Libya Janar khalifa Haftar ya yi barazanar cewa, sojojin kasar za su kwace iko da birnin Tripoli, matukar gwamnatin hadin kasa da ke da mazauni a birnin ba ta iya kawo karshen tashe-tashen hankula a birnin ba.

Rahotnni daga kasar ta Libya sun cewa, a yau Juma'a Janar Haftar ya yi wa gwamnatin hadin kasar Libya kashedin cewa, ya ba su wa'adin 'yan kwanaki da su kawo karshen tashe-tashen hankula a birnin, idan kuma ba haka sojojin kasar za su kwace iko da birnin baki daya.

Janar Haftar ya ce akwai 'yan bindiga da daa da suke dauke da muggan makamai a cikin birnin Tripoli, kuma suna iko da yankuna da dama na birnin, wanda hakan ke nuni da cewa sun fi karfin gwamnatin hadin kan kasar.

Haftar ya ce 'yan bindigar suna karbar umarni ne daga wasu kasashen ketare, kamar yadda kuma wasu daga cikin masu rike da mukamai suna tare da kungiyoyin 'yan bindigar, wanda a cewarsa hakan babban hadari ga kasar Libya.

Tags

Ra'ayi